Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutane 387 da suka sake kamuwa da cutar korona bayan gwaje-gwajen da aka gudanar ranar Juma’ar nan.

Hukumar wacce ta bayyana hakan a shafinta na twitter, ta ce yawan masu dauke da cutar yanzu a Najeriya ya karu zuwa dubu 9 da dari 3 da 2.

Hukumar ta ce an sallami mutane 105 da suka warke daga cutar, sannan kuma wasu biyu sun mutu sanadiyyar kamuwa da cutar.

A jihar Legas kadai mutane 254 ne suka sake kamuwa da cutar, sai babban birnin tarayya Abuja dake da mutane 29, a jihar Jigawa akwai mutane 24 da suka sake kamuwa da cutar sai jihar Edo dake da mutane 22.

Sauran jihohin sun hada da Oyo dake da mutane 15, Rivers 14, Kaduna 11, Borno 6, Kano 3, Plateau, Yobe, Bauchi da Gombe kowannen sun a da mutane bibbiyu, sai jihar Ondo dake da mutum guda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *