Ministan Yada Labarai
Lai Muhammad

Gwamnatin taerayya ta ce hukumar yake da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC sun kwato kudaden almundahana naira billiyan dari da 13, ciki har da kudaden kasashen ketare.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad, ya bayyana haka ga manema labarai lokacin ya yake zayyano irin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu.

Daga cikin kararrakin  da hukumomin 2 suka shigar kan almundahana ICPC ta yi nasara akan mutane 25, yayin da EFCC ta samu nasara a kan mutane 1,270 da ta shigar da karar su bisa laifin almundahana.

A bangaren tsaro, Muhammad ya ce matakin da shugaba Buhari ya dauke na rufe kan iyakokin kasa ya taimaka wajen rage yawan kashe-kashe da ‘yan ta’adda ke yi a baya.

Muhammad ya kara da cewa gwamnatin tarayya ba ta yi farin ciki da bullar cutar Korona a Najeriya ba, amma matakan da ta dauka sun taimaka wajen takaita wadanda suka kamu da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *