Mataimakin Gwamnan Borno

Gwamnatin jihar Borno ta ce an sallami mutane 135 da suka warke daga cutar korona bayan kwashe kwanaki suna jinya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Usman Kadafur, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar killace masu dauke da cutar daka Maiduguri.

Ya ce gwamnatin jihar ta samu gaggarumar gudunmawa a yaki da take da cutar korona.
Sannan ya yabawa ma’aikatan lafiya, hukumar lafiya ta duniya WHO, da kuma sauran wadanda suke taimakawa a yaki da gwamnatin jihar ke yi da cutar.

Mataimakin gwamnan wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar, ya ce hadin gwiwar da aka samu a tsakanin bangarorin ya taka muhimmiyar rawa a yaki da cutar.

Kadafur ya kuma shawarci al’ummomin jihar da su ci gaba da amfani da matakan kariya kamar yadda kwararru kan harkokin lafiya suka bukata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *