Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatin kasar India ta gaggauta daukar fansa ga dan Najeriya da aka daka har ta kai gay a rasa ransa a New Delhi dake kasar.

Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya dake kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci hakan a shafin ta na twitter.

Sannan ta bukaci ‘yan Najeriya dake zaune a kasar ta India su kwantar da hankulansu, yayin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, domin daukar mataki.

Wannan na zuwa ne bayan ofishin jakadancin Najeriya dake India ya kai kara ga rundunar ‘yan sandan kasar, domin a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce mutanen sun rufe dan Najeriyar mai suna Sunny Mike da duka ne a daidai lokacin da wata ‘yar kasar ta zargeshi da laifin sata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *