GWAMNAN KEBBI
ALH. ABUBAKAR ATIKU BAGUDU

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce babu mai ke ɗauke da cutar korona a jihar yanzu.

Kwamishinan lafiyan jihar, Jafar Mohamed Kilin, wanda shine shugaban kwamitin yaƙi da cutar a jihar, ya tabbatar da haka.

Ya ce an sallami mutane biyu da suka rage bayan gwaji ya tabbatar da cewa ba su ɗauke da cutar.

Bayanan hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar a baya ya nuna cewa mutane 33 ne suka kamu da cutar korona a Kebbi, tun bayan bullarta a jihar.

Sai dai keamishinan ya ce suna jiran samfurin wasu da suka aika domin tabbatar da ko suna ɗauke da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *