Gwamnan Kaduna
Nasir Ahman El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai, ya nuna damuwa bisa yawaitar ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

El-Rufai wanda ya bayyana haka a fadar shugaban kasa dake Abuja, ya ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, hakan zai iya shafar aikin gona.

Ya ce ya kai ziyarar fadar shugaban kasan ne domin tattaunawa tare da samar da mafita akan matsalar tsaro da taki ci taki cinyewa a yankin.

A cewarsa jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu wajen daukar matakan da suka kamata na yaki da ‘yan ta’addan.

El-Rufai ya kara da cewa maganar ayyukan ta’addancin jihar Sokoto shi yafi saukar hankalin jama’a, amma jihohin Kaduna, Niger da Katsina, sun dade suna fafutukar yaki da ayyukan ta’addanci tare da gudunmawar jami’an soji.

Sannan ya yabawa jami’an sojin sama da na kasa, bisa irin kokari da suke yi, da ma irin gudunmawar da jami’an sojin ruwa ke badawa a yankin kudancin Kaduna.

Gwamnan ya ce shugaban sojin sama na Najeriya ya bada tabbacin yin dukkanin abin da ya kamata na yaki da ‘yan ta’addan domin ba manoma damar ci gaba da aikin gonansu a lokacin da damina ke kankama.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *