Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin mambobin hukumar gudanarwar Kamfanin matatar man fetur na Ƙasa NNPC.

Mai taimakawa shugaban ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.

Ya ce shugaban ya amince da nadin nasu ne bayan cikar wa’adin hukumar gudanarwar da aka naɗa su a shekarar 2016.

Sabbin membobin hukumar gudanarwar sun haɗa da Mohammed Lawal, Tajudeen Umar, Adamu Mahmood Attah Magnus Abe, Dr Stephen Dike da kuma Cif Pius Akinyelure.

Wadanda aka nadan za su yi aiki ne a hukumar gudanarwar na tsawon shekaru uku.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *