Marigayi Maikanti Baru

‘Yan Najeriya na ci gaba da alhinin tare da mika ta’aziyyar tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya, Maikanti Kacalla Baru ya rasu.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, wanda ya tabbatar da rasuwar, a wani sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya yabawa halayen tsohon shugaban kamfanin.

An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da shekarar 1959 kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.


Ya soma aiki a kamfanin matatar mai na Najeriya ne a shekarar 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban kamfanin.


Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *