Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙara wa’adin shugabar riƙo ta Kotun Daukaka Ƙara ta ƙasar  Monica Dongban-Mensem.

A wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a ranar Juma’a, ta bayyana cewa sabon wa’adin na rikon kwaryar zai fara aiki ne daga 3 ga watan Yunin 2020.

An nada Mai Shari’a Monica a matsayin mai rikon kwarya ne biyo bayan ajiye aiki da Zainab Bulkachuwa ta yi, a daidai lokacin da ake shari’ar zaben shugaban kasa na shekarar da ta gabata.

Monica Dongban-Mensem ‘yar asalin Jihar Filato ce, kuma kafin nadin nata ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Enugu.

Ta yi karatun digirinta na farko da na biyu a bangaren shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *