‘Yan bindigan sun kai hari ne kwana daya biyo bayan ziyarar gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal inda yayi musu jajen kisan mutane goma sha hudu a ciki harda mai unguwar Gajt ranar Sallar Idi.

Kauyukan da aka kaiwa harin na baya-bayannan sun kunshi Garki, Dan Aduwa, Kuzari, Katuma da Masawa.

Shaidu sun bayyana wa manema labarai cewa mutane 40 akan babura dauke da makamai masu yawa sun kai farmaki akan kauyukan ne da misalin karfe uku na rana, inda suka ringa harbin mai kan uwa da yabi, lamarin da aka share sa’o’i yana gudana.

Wani wanda ya shaida kuma ya bukaci a sakaye sunansa yace “a halin yanzu da nake magana, mafi yawancin mazauna kauyukan sun gudu daga garuruwan su suna fargabar za’a sake kawo sababbin hare-hare, saboda maharan sun canza salo. A baya, dabbobi kawai suke kashewa ko su sace su, amma yanzu har mutane suke kashewa”.

“Biyo bayan harin, jama’ar kauyukan sun fara neman ‘yan uwan su. A halin yanzu, an samu gawarwaki saba’in; mutane ashirin da shida a kauyen Garki, da goma sha uku a kauyen Dan Aduwam, mutane ashirin a Masawa, da mutum takwas a Karina da kuma uku a kauyen Kazari.

“Wasu mutanen sun shiga daji domin neman ‘yan uwan su kuma har yanzu basu dawo ba. A hakan ma ba’a maganar wadanda suka ji ciwo saboda akwai mutane da yawa.

“Akwai mutanen da aka harba, sannan wasu da yawa sun karye, wasu kuma sun samu gocewar kasha yayin da suke kokarin tserewa daga hare-haren.

“Maharan sun kuma kashe mutane da yawa akan hanyar su na zuwa kauyukan. Sun kashe duk wanda suka gani akan hanya.” a cewar wani dan yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *