Miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka yi farin cikin hawan sa kujerar shugaban kasa a shekara ta 2015 a matsayin wanda zai ceto kasar daga matsalolin da take ciki.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

An yi masa wannan kyakyawan zaton ne saboda mulkin kama karya da yayi shekaru talatin da suka wuce a matsayin sa na shugaban mulkin karfin soja, wanda bai damu da abun duniya ba, inda yafi mayar da hankali akan da’ar alumma, sannan ya jure yunkurun juyin mulki daga ‘yan uwansa sojoji har ma ya share shekaru uku da tsare.

Duk da haka, ya samu nasarar zama shugaban Najeriya mafi magoya baya tun bayan jamhuriya ta farko, sannan ya jure tarkuna da kalubale iri iri na tsawon shekaru goma sha uku a matsayin shugaban ‘yan adawa, sannan a karshe ya samu damar cin galaba akan shugaban kasa dake kan mulki a karo na farko a tarihin Najeriya.

Tun bayan wannan lokacin, labarinsa ya canza kamar jirgin saman da fuka-fukinsa suka balle a tsakiyar ruwan sama a cikin dare. Har yanzu bai sauko ba, kuma bai fado ba. Amma akwai jan aiki a gabansa na ganin ya tuka wannan shagidadden jirgi zuwa inda ya kamata ya sauka ba tare da ya tarwatse ba.

A shekaru biyar din da yayi akan mulki, kyakyawan sauyin da ake kyautata zaton zai kawo ya ci tura. A gefe daya, yanayin siyasar da ya ke fuskanta yanzu ya sha bam-ban da lokacin da ya ke mulkin kama-karya a matsayin soja. Wancan lokaci, yana da kuruciya, yana da akida kuma baya daukar wargi.

Yayi mulki ne ta bada umarnin kai tsaye, kuma manufofinsa sun fi kundin tsarin mulkin kasa da kotu tasiri. Yana iya zabar gwamnoni da ministoci kai tsaye. Masu taimaka masa sune wasu sojoji ashirin da biyu wadanda ake kira Kwamitin Sojin Koli. A matsayinsa na shugaban farar hula a yanzu da yake mulki, kundun tsarin mulkin Najeriya na yi wa Buhari burki.

Sannan jam’iyyarsa kanta a rabe yake. Inda mafi yawancin ‘ya’yanta ba su amince da manufofinsa ba, sannan ga jam’iyyar adawa da ya gagara kalubalanta. Sai kuma Majalisar Wakilai da Dattijai masu tsawatarwa da ma zafafan kotunan kasa. Bugu da kari, akwai gwamnoni da jama’a ne suka zabe su.

Ga kuma tattalin arzikin kasa wanda ya canza inda kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu suka fi taka rawar gani, da kuma mataimakin shugaba wanda bai sani sosai ba. Yemi Osinbajo lauya ne, kuma limamin coci sannan babba ne a harkokin jami’a inda ya sha bam-ban daga Manjo Tunde Idiagbon.  

Buhari dai ya fara shugabancin sa ne da wani salo da ‘yan Najeriya basu zata ba, inda ya bayyana a jawabin sa na farko cewa shi mutum kowa ne, kuma shi ba na kowa bane. Amma ba’a jimawa, masu fashin baki suka shi mutum wata ‘yar karamar kungiyar kabal ce.

Duk da cewa an zargi duka tsofaffin shugabanni tun daga Shehu Shagari na cewa suna kewaye da mataimaka masu girman kai da rashin akida, Buhari yafi dukkanin su shan kazafin cewa yana zagaye da kabal. Ba kamar shekarun 1984 zuwa 1985 ba lokacin da yake tsare ‘yan siyasa da yawan su.

Inda yake zabar mukarraban gwamnati, da korar ma’aikata, da kuma gabatar da manufofi cikin hanzari kuma akai-akai, a wannan lokacin yayi kaurin suna a matsayin wanda yake daukar dogon lokaci kafin ya yanke shawara. Sai da ya share watanni uku kafin ya zabi sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Sannan ya share watanni uku kafin ya zabi manyan shugabannin soji, da kuma kusan wata shida kafin ya zabi ministoci. Ya share watanni da yawa yana sauraron rahotanni daga sakatarorin gwamnati, inda manyan hukumomi da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati suka share shekaru ba tare da shugabanni ba.

Buhari ya share shekaru biyu bai zabi jakadu ba, sannan manyan ma’aikatun gwamnati da yawa sun share shekaru ba tare da shugabanni ba. An dan samu cigaba a shekara ta 2019 bayan sake zabar sa, amma ba’a ga tsari ba kamar na Amurka inda shugaba yake zabar ministoci kafin a rantsar da shi.

Idan an lura kuma, za’a ga cewa dangantakar Buhari da majalisun kasa guda biyu bata da danko a shekaru hudun sa na farko. ‘Yan Najeriya da yawa sun kalli rigima tsakanin Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara a matsayin abunda bai kamata ba tunda duka mutanen biyu ‘yan APC ne.

Lamarin yayi tsami har ta kai ga fadar shugaban kasa ta fara zargin majalisun da kara kudi a cikin kasafin kudin kasa, da cin hanci da hana ruwa gudu wajen gudanar da ayyuka. To duk da cewa shugabanin majalisun kasar su biyu duk suna goyon bayan Buhari, hakan bai taimaka wajen ayyana doka da manufofi ba akan lokaci. Dangantakar Buhari da bangaren shari’ar kasa itama bata da dadi.

Akwai lokacin da yake tattaunawa da ‘yan Najeriya dake Kenya a shekara ta 2016 yana mai cewa masu gudanar da shari’ar kasa na hana ruwa gudu wajen yaki da cin hanci da rashawa. Haka zalika zuwan bazata da jami’an DSS suka kaiwa Manyan Alkalan Kotun Koli na kasa, da tsawwala wa Alkalin Koli Walter Onnoghen ya kara dagula lamari. Shi kan shi dangantakar Buharin da jam’iyyar shi ta APC na da matsala babba.

Matsaloli da suka kalubalanci PDP da ta dade tana mulki sun saka wasu daga cikin ‘ya’yanta masu muhimmanci tserewa zuwa APC a shekara ta 2013 lokacin da aka kirkiro ta. A cikin su harda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu gwamnoni wadanda suka zo daga abunda suka kira nPDP.

To a shekara ta 2015, Buhari yayi siyasar SAK, wato a zabi duk wani dan jam’iyyar APC. Wannan lamari ya kawo wa APC nasara amma yanzu alamu na nuna cewa yayi nadamar haka. A kowace rana, APC na kara kama da PDP, saboda haka Buhari yana kara nisantar kanshi daga jam’iyyar.

Yanzu dai idan aka kula, za’a ga baya nuna wani damuwar shi da jam’iyyar inda ya bar jam’iyyar ta zama abunda take son zama, kuma sai ya share watanni bai yi zaman shugabannin jam’iyya ba ko ya hallarci manyan tarurruka.

Kwamitin Aikin APC na kasa shima ya samu kanshi a cikin wani yanayi mara dadi inda ya share sama da shekara daya yana kokarin sauya shugabanin ta kamar Sakataren Kasa amma abun ya gagara.

Daga baya ta dakatar da manyan jami’anta na kasa da jihohi, amma kotu da dawo da su saboda ba’a bi ka’ida ba. Duk da cewa Buharin ya samu nasara cikin sauki a lokacin zaben 2019, APC kuwa ta ci kwakwa.

Duk da dai ta samu nasarar rike jihar Osun, da ciwo Ekiti da Ondo da Kwara da Oyo daga hannun PDP, ta rasa Bauchi da Adamawa, kuma na kusa rasa Kano, kuma da kyar ta rike Kano da Ogun, amma bata samu damar kwato Benuwe da Sokoto ba daga gwamnonin APC da suka sauya sheka.

Haka kuma ta rasa Zamfara saboda fadan cikin gida, ta rasa Imo amma kotu ta dawo mata da ita. Ta kuma ciyo Bayelsa, amma kotu ta kwace ta baiwa PDP. Dangantakar Buhari da kafafen yada labarai na kwan-gaba-kwan-baya.

‘Yan jarida na yiwa shugaban kallon wanda ya nesanta kanshi da jama’a, kuma bai iya bayyani ba. Ba kamar Obasanjo ba, Buhari kusan baya ganawar tattaunawa da manema labarai, da kyar yake hira da ‘yan jaridar Najeriya. Sannan yana bayyana mafi yawancin manufofinsa masu muhimmanci a kasashen waje a tattaunawa da ‘yan Najeriya da ke zama a wadannan kasashe da yake kaiwa ziyara.

A bangaren shugaban kuma, shi da manyan jami’an sa nayi wa ‘yan jarida kallon wadanda suka lalace daga cin hanci da rashawa kuma suna sukar su ne, saboda ba kamar shugabannin baya ba, basa basu kudin goro.

Haka zalika, ‘yan jarida na kallon Shugabancin Buhari a matsayin marar da’a, inda manyan jami’anta ke cikin fada ko yaushe, Kamar Ministan Mai Ibe Kachikwu da Manajan NNPC Maikanti Baru, da kuma tsakanin Kachikwu din da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Marigayi Abba Kyari, da tsakanin Abba Kyari da Shugaban Ma’aikata Eyo-Ita, da kuma tsakanin Kyari da mai baiwa shugaban kasa shawara Janar Monguno.

Da kuma tsakanin shugaban EFCC Ibrahim Magu da daraktan DSS Lawal Daura, da tsakanin shugaban APC Adams Oshiomhole da mambobin Kwamitin Aikin APC, wato tsakanin Oshiomole da Gwamna Yari, Okorocha, Amosun da Obaseki, da tsakanin ministan Sadarwa Isa Pantami da shugaban hukumar kula da sadarwa Farfesa Danbatta, da kuma tsakanin Pantami da shugabar ma’aikatar ‘yan kasa dake kasashen ketare Abike Dabiri Erewa.

Sai kuma batun Abdulrashin Maina inda aka kori shuganan hukumar Fansho, amma aka dawo da shi shugabanci a sirrance, inda abunda ya jawo wa gwamnatin kunya, har ta kai ga cece-ku-ce a fili tsakanin Kyari da Eyo-Ita. An kuma samu damuwa inda matar shugaba Buhari, Aisha Buhari ta fara kai hare-hare akan mutanen da ake cewa suna kewa da mijinta akan harkokin shugaban ci.

Wannan ne yasa Buharin ya fadi abun kunya a bainar jama’a a kasar Jamus, inda yace matar tasa ta tsaya a dakin dafa abinci, ko a can daya dakin. Dangantakar Buhari da ma’aikata itama bata da lafiya tun shekara ta 2016 saboda kara farashin man fetur, yajin aiki daga kungiyoyin kwadago na fannin ilimi, da lafiya da shari’a, da kuma tafiyar hawainiya da aka yiwa kara mafi karancin albashin da za’a baiwa ma’aikata bayan kaddamar da shi.

Alamu sun nuna cewa bashi da wani shiri akan lamarin, sannan yayi kokarin aiwatar wa ta amfani da EFCC a mafi yawancin lokaci. Shugaban EFCC din Ibrahim Magu wanda har yanzu Majalisar Dattijai bata amince da shi ba, yana da zafi wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Mafi girma daga cikin aikin da yayi shine bankado satar kudaden makamai, da gagarumin cin hanci da rashawa a bangaren mai, da kuma wani katon cin hanci da aka gudanar domin cin zabe wanda aka zargi tsohuwar Ministan Mai Diezani Allison Madueke. Duk da cewa an samu wasu daga ciki da laifi, har yanzu manya-manyan shari’o’i da yawa suna makale a kotuna.

Shugabannin PDP suma sunce ana zabar wanda za’a bincika ne a yaki da cin hanci da rashawa, sannan ana yafewa duk wani dan PDP da ya sauya sheka ya koma APC, a wata subutar baki da Oshiomhole yayi.

Duk da cewa an kwashe shekaru biyar inda batun yaki da cin hanci da rashawa shine mafi muhimmanci a cikin manufofin shugaban, matsayin Najeriya bai samu wani cigaba ba rahoton duniya da ake fitarwa dangane da kasashen da suka fi fama da satar kudaden gwmnati.

Ana kyautata zaton cewa wannan ya zo ne daga cin hancin da ake yi a ma’aikatun gwamnati, da harkokin tsaro, da fannin shari’a, da siyasa da ma zaman rayuwa na yau da kullum.

Duk da cewa yayi kokarin neman gudanar da wasu manya-manyan ayyukan da zasu kawo kayan more rayuwa ga ‘yan kasa kuma ya bayyana shirin biliyoyin nerori na kawo cigaban rayuwar ‘yan kasa, alamu na nuna cewa Shugaba Buhari bashi da wani takamaiman tsarin gina tattalin arzikin kasa.

Turjewar tattalin arzikin shekara ta 2015 zuwa 2017 da ya samo asali daga faduwar farashin mai ya kawo wa Buhari kalubale dun kafin yayi nisa a shugabancin nasa. Manyan masana tattalin arziki sun bayyana cewa zai iya kalubalantar matsalar a wannan lokaci da ya dauki matakan da suka dace.

Sai dai Buhari bashi da mai bashi shawara akan tattalin arziki a bayyane. A wa’adin sa na farko, ya dora wa mataimakin sa Osinbajo alhakin zama shugaban kwamiti tattalin arziki na kasa.

Amma a shekarar da ta gabata, an karbe wannan aiki kuma an baiwa Kwamitin bada shawara akan tattalin arziki, kuma har yanzu wannan kwamiti bai fitar da tsari ko daya akan yadda za’a tafiyar ta tattalin arzikin Najeriya. Saboda haka, a shekaru biyar, akwai manya-manyan kalubalen tattalin arziki da wahalhalun rayuwar kasa da yawa da har yanzu ba’a takala ba.

A cikin su akwai rashin wutar lantarki, rashin ayyukan yi, tashin farashin nera da lalacewar darajar ta, da lalacewar matatun man Najeriya hudu lamarin da yasa Najeriya ta koma dogara akan mai daga kasashen waje.

Yawan fita waje da shugabanni da masu arziki suke yi domin kiwon lafiya bai taimaka wa bangaren kiwon lafiyar Najeriya ba. Rashin tsaro babban kalubale ne a shekaru biyar din da Buhari yake shugabanci. A matsayinsa na Janar wanda yayi fada a yakin basasa, mutane da yawa sun yi zaton Buhari zai kawo karshen Boko Haram a cikin dan karamin lokaci.

Duk da sauye-sauyen tsarurruka na sojoji da kudade da aka samar domin sayan makamai, har yanzu ba’a kammala cin ‘yan ta’addan da yaki ba. A makonnin da suke gabata, rundunar sojoji da Laftanar Janar Buratai ke jagoranta na nuna alamun samun galaba akan mayakan.

Tabarbarewar tsaro a cikin kasar baki dayan ta, musamman masu garkuwa da mutane da kashe-kashen mutanen kauye da satar kayan su a arewa maso yammacin kasa, yanzu ya zarta yaki da Boko Haram a matsayin batun tsaro mafi muhimmanci a kasa.

Arangama na jina-jina da ake cigaba da yi tsakanin makiyaya da manoma a jihohin tsakiyar Najeriya, da fadace-fadace tsakanin al-ummomi a jihohi da daya, da rashin tsaro a yankin kudu maso yammacin kasa sun kawo wa kawo wa gwamnatin Buhari tsaiko, kuma hakan ya sa jama’ar kasa na sukan ta.

Bugu da kari, lafiyar Buhari itama ta zama babbar batu a lokacin da ya share watanni takwas a wani asibitin kasar waje a shekara ta 2017. Buharin dai na cigaba da shan suka saboda bai cika alkawuran da yayi ba lokacin da yake yakin neman zabe, musamman bayyana kadarorin sa, da sayar da jiragen gwamnati da kuma gujewa asibitocin kasashen waje.

Duk da cewa fadar shugaban kasa na gardamar cewa an fi zabar mutanen kudancin kasa a kujerun gwamnati, har yanzu ana cigaba da zarginta da nuna bangaranci. A shekarun farko, an samu dangantaka aiki mai kyau tsakanin Buhari da mataimakin sa Osinbajo.

Amma dangantakar ta lalace a shekarar da ta gabata biyo bayan rage ma’aikatan Osinbajon da aka yi, aka karbe wasu ayyukansa, sannan aka mika wasu manyan ma’aikatun gwamnati da yake jagoranta zuwa ga wasu sababbin ma’aikatun. Yanzu haka ba’a cika ganin Osinbajo a bainin jama’a ba.

A kwanakinnan, mafi yawancin sukar da aka yiwa shugabancin Buhari shine na cewa marigayi, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa na da karfin iko fiye da yadda ya kamata. A watan Agustan da ta gabata ne, Buhari ya umarci duka ministoci akan su gana da shi amma ta karkashin Kyari.

Biyo bayan rasuwar Kyari a watan da ya gabata, Buhari ya zabi wani dan boko wanda ake girmama wa kuma jami’in diflomasiyya Ibrahim Gambari a matsayin wanda ya maje gurbin Kyari. Har yanzu dai ba’a san alkiblar Gambari ba a siyasance, sannan ba a san yadda shugabancin Buharin zai kasance ba, biyo bayan zaben Gambarin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *