Jirgi na farko ya sauka a sabon filin sauka da tashin jiragen saman dakon kaya na jihar Yobe dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnan jihar Mai-Malah Buni da tawagarsa suka tarbi jirgin da ya taso daga filin jiragen sama na Nnamdi dake Abuja.

Tsohon gwamnan jihar Ibrahim Geidam ne ya dasa tubalin ginin filin jirgin, wanda gwamna Buni ya ci gaba da aikin da ake kyautata zaton zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da ma Najeriya baki daya.

A lokacin tarbar jirgin farkon, gwamnan ya ce filin zai iya saukar jiragen dakon kaya daga ko ina a kasashen duniya.

Wasu masana tattalin arziki sun yabawa gwamnan jihar bisa ci gaba da aikin, wanda a cewarsu zai taimaka sosai ta fuskar kasuwanci.

Ra’ayoyi 2

Your email address will not be published. Required fields are marked *