Abubakar Malami
Ministan Shari’an Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce duk gwamnan jihar da ya taba ‘yan Majalisun dokokinsa da bangaren shari’a, zai rasa kason kudaden da jiharsa ke samu.

Ministan shari’a, kuma babban Antoni Janar na tarayya Abubakar Malami ya yi gargadin a Abuja.

Ya kuma kara da cewa duk jihar da aka samu da kin warewa wadannan ma’aikatun kudaden su, za a ba akawun kasa umarnin zare kudaden tun daga kason da jihar ke samu daga tarayya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *