Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umurci rundunar sojin Najeriya da ta gaggauta murkushe ‘yan ta’addan da suka dade suna bar na a jihar Sokoto.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya

Shugaba Buhari ya bada umurnin ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu.

Ya ce gwamnatin tarayya na iya bakin kokarin ta wajen samar da zaman lafiya da tsaro, wanda hakan ya sa aka kaddamar da runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.

Bayanin shugaban na zuwa ne bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake karamar hukumar Sabon birni dake jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama tare da tilastawa karin wasu tserewa daga gidajensu.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *