Kididdigar hukumar NCDC kan masu korona a Najeriya

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutane 389 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Hukumar ta ce a jihar Legas kadai mutane 256 ya yin da jihar Katsina ke bi mata da mutane 23, Edo na da mutane 22, sai Rivers dake da mutane 14, Kano 13.

A jihohin Adamawa da Akwa Ibom akwai mutum 11 ko wannen su. Kaduna akwai mutane 7, sai mutane 6-6 a jihohin Kwara da Nasarawa. Haka kuma an samu mutane bibbiyu a jihohin Gombe, Plateau,

Abia, Delta, Benue Niger da Kogi. Sai jihohin Imo, Borno, Ogun da Anambra dake da mutum dai-dai. Hukumar ta ce yanzu akwai mutane 8733 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Sannan mutane 2501 sun warke, baya ga 254 da suka rasa rayukansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *