Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya aikewa majalisar wakilai wasiƙar neman amincewarta da ta da karbo bashin Dala Biliyan 5.513 da ga waje dimin cike gibin kasafin kudin shekarar 2020.

Shugaban Majalissar Femi Gbajabiamila ya karanta wasikar a zaman Majalissar.

A cikin wasiƙar, shugaba Buhari ya ce za a karbo rancen ne daga, Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, Bankin Duniya, Bankin Cigaban Afirika, Bankin Cigaban Musulunci, Bankin Shiga da Fitar da kaya na Brazil, da kuma Bankin Shiga da Fitar da kaya na Afirika.

Ya kara da cewa idan aka aro kudin za su tallafawa Gwamnonin jihohi domin fuskantar kalubalen da ake fama dashi na annobar Korona da aka fi sani da Covid19.

Majalisar ta kuma mika takardar ga Kwamitinta dake kula da basussuka domin tattaunawa da kuma duba yiwuwar amincewa da bukatar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *