Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Hoto: Gidan Gwamnati

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da fitar da kudi, a karon farko, domin fara aikin samar da wutar lantarki da aka kulla yarjejeniyarsa da kamfanin SIEMENS.

Tun a cikin shekarar 2019 shugaban kasa ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tare da kamfanin domin kara adadin karfin wutar lantarkin kasa da megawat dubu 7 zuwa shekarar 2021.

A jerin wasu sakonni da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na tuwita, shugaba Buhari ya bukaci ma’aikatar lantarki da ma’aikatar kudi su kammala dukkan wani shiri domin fara gudanar da aikin.

Shugaba Buhari ya ce burinsa shine samar da wutar lantarki a kasa domin amfanin gidaje da kamfanoni.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *