Gwamnatin Najeriya ta ce za ta mai da otel-otel da makarantu wuraren killace masu dauke da cutar korona.

Dr. Osagie Ehanire
Ministan Lafiya

Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya tabbatar da haka a lokacin da yake jawabi a taron kwana guda-guda da kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin yaki da cutar Korona.

A cewarsa ana ci gaba da korafe-korafe akan karancin gadajen kwantar da masu dauke da cutar korona, a daidai lokacin da masu cutar ke kara yawa a Najeriya, musamman Legas.

Sannan ya bada tabbacin cewa karancin gadaje da ake samarwa masu dauke da cutar ba zai zama matsala ba, kamar yadda aka rika gani a wasu kasashen duniya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *