A daren Laraba ne gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Tumur dake Jihar Diffa a Janhuriyar Nijar inda ta lakume gidaje 500.
Abunda ya rage kennan daga sansanin ‘yan gudun hijira na garin Tumur bayan gobara ta kona komai da komai. Hoto: Gambo Meleh Bujih

Ya zuwa yanzu ba’a san dalilin gobarar ba, amma ta share sama da sa’a daya tana ci inda ta kone mazaunin ‘yan gudun hijira har kasa kuma mutum daya ya rasa ransa.

‘Yan gudun hijirar sun komo Tumur da zama ne daga kauyuka daban daban a ciki har da Abadem sakamakon fitinar Boko Haram.

Wani mazaunin sansanin mai suna Gambo Meleh Bujih ya bayyana cewa ya zuwa lokacin buga wannan labarin, babu hukuma ko jami’in gwamnati da ya kai musu dauki, amma suna san ran zuwan gwamnan Jihar.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *