Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni (a dama) da Babban Hafsan Sojin Saman Air Mashal Najeriya Sadique Abubakar (a hagu)
Hoto: Mamman Mohammed

Sabuwar tashar sauka da tashin jirgin sama masu saukar Ungulu a jihar Yoben Najeriya ta shirya yin gwajin sauka da tashin jirgin farko a ranar Jumma’a mai zuwa a cewar Gwamnan Jihar Mai Mala Buni.

Gwamnan ya bayana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin hafsan hafsoshin sojin saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar a wata ziyarar aiki da ya kai a garin Damaturu. Mai Mala Buni ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari da hafsoshin soji da sauran dakarun sojoji kan nuna kwazon kawo karshen ta’adanci.

Ya kuma bada tabbacin gwamnatinsa ta jihar Yobe wajen bada gudumawa ga jami’an domin samun zaman lafiya a jiha. Gwamna Buni ya kara da cewa, samun zaman lafiya yanzu a jiha, ya sa an yi bukukuwan sallah lafiya.

Air Marshal Abubakar Sadique ya yaba da kokarin Gwamna wajen taimakawa jami’an tsaro. Ya kuma ce, sabon filin saukar jirage masu saukar Ungulun da a ka yi a Damaturu zai taimaka matuka kan yaki da ta’adanci a jihar Yobe. Sadique ya ce sojin sama sun dukufa kwarai wajen kawo karshen ta’adanci a Nijeriya.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *