Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce yawan dakunan gwaje-gwajen cutar Korona ya karu zuwa 28 a fadin Najeriya.

Hukumar wacce ta bayyana hakan a shafin ta na twitter, ta ce an samu karin cibiyoyin gwajin cutar 2 a jihohin Katsina da Ogun. Hukumar ta kara da cewa baya ga guda biyun da aka kaddamar, akwai karin wasu da ake gaf da gama aikin su a jihohin Gombe da Kwara.

A baya dai babban daraktan hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Ghebreyesus, ya ce babu tabbaci akan adadin masu dauke da cutar a Afrika, saboda karancin wuraren gwaji da nahiyar ke da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *