‘Yan Majalisun Dokokin Najeriya a bakin aiki

Majalisun dokoki na Najeriya za su koma bakin aiki a gobe Alhamis bayan kammala hutun karamar Sallah domin tattaunawa akan gyare-gyaren kasafin kudin 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike musu.

Magatakardar majalisar dattawa Mohammad Sani Omolori ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Ya ce ana sa ran ‘yan majalisar dattawa da wakilai za su koma bakin aiki domin tattaunawa akan gyare-gyare da shugaba Buhari ya yiwa kasafin kudin.

A ranar 20 ga watan Mayu ne majalisun biyu suka tafi hutun karamar Sallah tare da kudurta cewa za su dawo bakin aiki a ranar 2 ga wata mai zuwa. A baya ma shugaban majalisar dattawa ya ce majalisun za su iya katse hutu domin komawa tare da yin aiki akan duk wani muhimmin abu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura musu, musamman ma kasafin kudin 2020.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *