Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya
Hoto: Ofishin Sakataren Gwamnati

Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta sake bude makarantu nan ba da dadewa ba. Ya bayyana haka ne a taron manema labaran da ya ke gudanarwa a kowace rana, domin wayar da kan al’ummar kasa game da cutar Korona.

Boss Mustapha ya ce kara da taya yara murnar ranar yara ta duniya da a ke murnar zagayowar ta duk ranar 27 ga watan Mayun ko wace shekara. Sannan ya kuma tabbatar wa iyayen yara da masu ruwa da tsaki cewa suna kokarin daidaita lokacin da ya dace domin bude makarantu.

Ya rufe da cewa Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Ilimi za ta fitar da matakan bi domin buɗe makarantu a faɗin kasar nan ba da jimawa ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *