Gwamnatin jihar Kaduna dake Arewacin Najeriya ta tsawaita dokar hana zirga-zirgar jihar da karin makwanni biyu a kokarin dakile yaduwar cutar korona a ciki da wasu yankunan jihar. Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai ne ya sanar da haka ta bakin mataimakiyarsa.

Hadiza Sabuwa Balarabe ta ce, an tsawaita dokar ne biyo bayan tattara shawarwari da kwararru kan harkokin lafiya a daidai lokacin da aka kwashe kwanaki sittin da sanya dokar. To amma an sami karin rana daya a kan ranaku biyu da jama’a ke fita a duk mako. Inda yanzu za su dinga fita ranakun Talata da Laraba da kuma Alhamis.

Hadiza ta ce kara wa’adin dokar bai rasa nasaba da irin karin shirye-shirye da jihar ke yi na sake bude harkokin yau da kullum tare da bada cikakkiyar kariya ga al’ummar jihar. Ta kara da cewa makarantu, wuraren ibada da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe, ya yin da za a rika tattaunawa da malamai, jami’an gwamnati, masarautun gargajiya, kungiyoyin sufuri da sauransu. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *