Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Hoto: @bashirahmad

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci zaman lafiya da hadin kan kasashen Afrika domin samun ci gaba mai dorewa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a sakon da ya aikewa shugabannin kasashen Afrika na zagayowar ranar Nahiyar na shekara ta 2020 da kungiyar tarayyar Afrika tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya WHO suka shirya.

Ya ce akwai bukatar dukka shugabannin kasashen Afrika su yi iya bakin kokarinsu wajen dakile yawan rikice-rikice da ake samu a Nahiyar, musamman ta hanyar wayar da kan al’umma kan alakar da ke tsakanin zaman lafiya da ci gaban kasa.

Shugaban ya kara da cewa zaman lafiya, tsaro, da diflomasiyya tare da fahimtar juna sune ginshikin ci gaban Afrika. Sannan ya bukaci bangarori masu zaman kansu, da kungiyoyi su maida hankali wajen yin amfani da irin wadannan lokuta domin tabbatar da zaman lafiya a kasashen Nahiyar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *