Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya

Majalisar zartarwa ta Najeriya ta bukaci ‘yan Najeriya da su dauki hadduran dake tattare da cutar korona da muhimmanci, tare da daukar matakan kariya da gwamnatoci ke badawa.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a cikin sakon barka da Sallah da ya aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, da sauran ‘yan Najeriya baki daya.

A cewarsa, akwai akwai bukatar ‘yan Najeriya su rika daukar matakan kariya da kawunansu, wanda hakan ne zai taimaka wajen yaki da annobar ta Korona a duniya.

Ya ce addu’ar majalisar zartarwar ne bisa Allah Ya amshi ibadu da kuma addu’o’i  musamman a irin wannan lokaci da kasashen duniya ke fafutukar yaki da cutar mai sarke numfashi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *