Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriya (INEC) ta bayyana cewa zata fito da sabuwar hanyar jefa kuri’a ta amfani da na’ura a shekara ta 2021.

Ta bayyana hakan ne a wata takarda mai taken “Manufofi Dangane da Gudanar da Zabe duba da Yanayin Annobar COVID-19” mai shafuka goma sha bakwai a birnin Abuja Litinin dinnan wadda shugabanta Farfesa Mahmood Yakubu ya sakawa hannu.

Manufofin sun kunshi batutuwa akan kiwon lafiya, da shari’a, da shirya zabe da gudanar da shi, aikin ranar zabe, da ayyukan bayan zabe, da rijistar zabe, da jam’iyyun siyasa, da lura da zabe, da tabbatar da tsaro a lokacin zabe da kuma amfani da fasaha domin gudanar da zabe a yanayin COVID-19.

Ta kara da cewa zata yi amfani da yanar gizo wajen karbar takardar rijistar ‘yan takara a zaben gwamnoni na Jihohin Edo da Ondo dake tafe. Hukumar tace zata fara gwada wannan sabon tsari a wasu zabukan kafin ta aiwatar da shi a kasa baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *