Sabon shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya fara gudanar da aikin sa a fadar Aso Rock.

Gambari wanda ba bako bane a gwamnatin Buhari, an dauko shi ne daga mukamin wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya kuma Ministan harkokin waje a gwamnatin Buhari.

Biyo bayan fara aiki ran sha uku da ga watan Mayu, aikin sa na farko shine zama a ganawar Kwamitin Zartaswa ta kasa da shugaban kasa ke jagoranta. A halin yanzu, ya hallarci irin wannan ganawa har sau biyu.

Jim kadan bayan ganawar, Farfesan ya kai ziyarar zumunci zuwa ofishin mai baiwa shugaban kasa Shawara akan harkokin Tsaro Manjo Janar Babagana Monguno.

Masu fashin baki sun bayyana cewa wannan abu ne mai kyau, saboda a baya ba’a samu jituwa ba tsakanin marigayi Abba Kyari da Monguno, inda Mongunon yake cewa ana yi masa katsalandan a harkokin tsaro.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *