Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kaso 1.87 cikin 100 a watanni hudu na farko a shekarar nan ta 2020, lamarin dake nuna tsukewa ta -0.68 cikin 100 idan aka kwatanta da 2.55 cikin 100 da aka gani a watanni hudu na karshe a shekara ta 2014.

Takardar rahoton da Ofishin Lissafin Kasa (NBS) ya fitar Litinin dinnan akan watanni hudu na farko a 2020 ya nuna raguwar bunkasar tattalin da -0.23 cikin 100 idan aka kwatanta da karuwar 2.28 cikin 100 da aka samu a watanni hudu na farko a shekara ta 2019.

Rahoton ya dora alhakin raguwar tattalin arzikin ne akan tsaiko da annobar cutar Korona ta jawo, da faduwar farashin man fetur da kuma raguwar cinikin kasa da kasa.

Ida nana biye, Najeriya kasa ce wadda ta dade tana dogara akan kudaden shiga daga sayar da man fetur, to amma a baya farashin ya fadi, lamarin da ya rage kudaden shigar kasar, da kuma lalacewar darajar Nera.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *