Kifaye iri iri ne suka riga mu gidan gaskiya a Kano, biyo bayan kwarara gurbataccen ruwan rini a cikin rafin Wudil.

Alhaji Lawan Wudil wanda shine wakilin hakimin Wudil ya gaya wa manema labarai Alhamis dinnan cewa wannan shine karo na farko a cikin shekaru da aka gurbata ruwa har ta kai shafar dabbobin ruwa, lamarin da ya jawo hankalin hukumomi.

Ya bayyana cewa gurbatattun sinadarai daga masana’antun rini da aka zuba a cikin rafin misalin karfe sha biyu na dare Asabar din makon da ya gabata ya kashe kifaye iri iri a cikin ruwan.

Ya kara da cewa mazauna garin sun yi ta kwasar kifayen da suka mutu, ba tare da sanin illar da kifayen zasu yiwa lafiyar su ba.

“Wannan lamarin yana da hadari sosai ga lafiyar jama’ar Wudil, saboda mutane da yawa sun dogara ne akan rafin domin rayuwa” inji Lawan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *