Majinyata dake fama da cututtuka iri iri a duk fadin Najeriya sun bayyana cewa jinya a gida saboda annobar cutar Korona ya jawo tabarbarewar lafiyar su. ‘Yan Najeriya da yawa ne suka koma yiwa kawunansu magani a gida musamman domin kare kawunansu daga COVID-19 a maimakon zuwa asibitoci.

Jami’ai da asibitoci sun bayyana cewa ana samun karuwar jama’ar dake fama da tabarbarewar lafiya, wasu ma har suna mutuwa sakamakon yanke shawarar zama a gida suyi jinyar kansu, a maimakon zuwa asibiti domin kwararre ya duba su.

Daruruwan mutane dake fama da hawan jini, da ciwon suga, da ciwon koda, da ciwon zuciya, da cutar daji, da zazzabin cizon sauro, da taifod na daga cikin wadanda ke fuskantar kalubale sosai a gida yayin da suke wa kawunan su magani.

A halin yanzu annobar cutar Korona na kalubalantar duka duniya baki daya, inda gwamnatoci da jami’an kiwon lafiya suke ta kokarin dakile yaduwar cutar, wadda samo asali daga kasar Sin. Ya zuwa yanzu Amurka tafi kowace kasa adadin mutanen da suka kamu da ita, da kuma mutuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *