Ofishin Hukumar Tantance Inganci Abinci Da Magunguna ta Najeriya
Hoto: Twitter @NafdacAgency

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tantance wasu kamfanoni da suka bayyana cewa sun samo magungunan gargajiya na rigakafi da kuma magance cutar Coronavirus. Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora, ya tabbatar da haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Kamfanonin sun gana da hukumomin ma’aikata da cibiyoyin kula da kuma tantance magunguna na gwamnatin tarayya. Bayan tattaunawar da suka yi an umurci kamfanonin su gabatar da samfurin magungunan ga hukumar tantance inganci abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, domin tantancewa tare da daukar wadanda za a yi amfani dasu wajen gwaji.

Ya ce an kuma gana da wakilan hukumar NAFDAC, da na cibiyar binciken magunguna, da kuma kungiyar masu sarrafa magunguna ta Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *