Kunguyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a jihar Ogun, tayi barazanar hawa sama da kamfanonin hakon ma’adanai inda tace sun mayar da ma’aikatan Najeriya kamar dabbobi.

NLC ta bayyana damuwar ta, tana cewa da yawa daga cikin kamfanonin hakar ma’adanai daga kasar China bata kula da ma’aikatan Najeriya, kuma bata bin yarjejeniyar aiki daka amince akai, inda take abunda ake kira “yin amfani da ma’aikata da jefar da su kamar bola”.

Shugaban NLC na Jihar, Emmanuel Bankole ya bayyana haka ne a karshen makonnan a ganawa da yayi da wakilan kamfanonin hakar ma’adanai a shedkwatar NLC dake birnin Abeokuta.

Ganawar wadda Kungiyar Ma’aikatan Hakar Ma’adanai (NUMW) ta shirya ta samu hallartar Komturola na Kwadago Kwamared Anthony Olawoyin, da shugaban Mahaka na Kasa, Bunmi Ayelabola da kuma shugaban NUMW na jihar Kwamared Fasiu Abiola.

Shugaban NLC da masu aiki a mahakar sun bayyana cewa babu kula mai kyau a kamfanonin, kuma ba’a samar wa ma’aikata kayan kiyaye lafiya ba a lokacin aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *