A jihar Sokoto, gwamnan jihar Aminu Tambuwal tare da sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar sun gudanar da Sallar Idi a Masallacin Sultan Bello. Sun saka takunkumi kuma sun ware tsakanin su da juna a lokacin da ake gudanar da Sallar Idi

Sai dai akwai sharuddan da aka saba dangane da sallolin, na hana mata da yara zuwa Sallar Idi, saboda akwai mata da yara da yawa da suka hallarta.

A jihar Borno, gwamna Babagana Zulum yayi iya bakin kokarin sa wajen bin umarnin da aka gindaya na warewa daga sauran jama’a da kuma saka takunkumi a lokacin da ake sallar Idi.

Babban Limamin Jihar, Shettima Mamman Shettima Salehi shine ya jagoranci Sallar tare da hallartar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi da sauran manyan mukarraban gwamnati.

An gudanar da Sallar ne a dandalin Ramat dake iya daukar dubban jama’a.

A garin Jos kuma, masu tafiya Sallar Idi sun gamu da ruwan sama mai nauyi. An samu jama’ar da suka saka takunkumin rufe baki da hanci, amma basu ware daga juna ba.

A babban birnin jihar Adamawa, Yola, an gudanar da Sallar Idi ne a Masallatan Juma’a domin rage cunkoson jama’a, amma mutane kadan ne suka saka takunkumi, kuma jama’a sun jera kafada da kafada da juna a lokacin gudanar da Ibadan.

A jihar Kano, dubban Musulmai ne a cikin su harda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Aminu Ado Bayero suka yi Sallar Idi a ware.

A lokacin gudanar da Sallar Idi, hukumar Hisbah ta jagoranci shirya mutane domin tabbatar da tsaron lafiya ga jama’ar dake hallartar Sallar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *