Assalamu alaikum, muna farin cikin bayyana muku cewa mun baku damar samun horon koyi daga kwararru na ‘internship‘ a turance tare da gidan Radiyon Talaka domin zama wakilanmu.

A wannan tsarin na internship, babu albashi ko alawus. Muna bukatar sanin wani irin aikin jarida ne yake baka/baki sha’awa, yadda zamu hada ka/ki da wanda ya dace a cikin kwararrun ‘yan jarida domin gudanar da horo.

Wannan internship za’a fara shi 1 ga watan Yunin shekarar nan ta 2020, kuma za’a ringa zabar duk wanda aikinsa yayi kyau sosai domin kara masa matsayi zuwa reporter. Daga reporter, matsayi na gaba shine Senior Reporter inda albashi ke farawa, daga nan sai Editor, sannan Managing Editor.

Abubuwan da ake bukata domin shiga wannan shirin internship sune:

  1. Takardar Kammala Sakandari
  2. Iya karatu da rubutun Hausa da bin dokokin rubutu.
  3. Kaunar aikin jarida.
  4. Juriyar jajircewa a wajen aiki.
  5. Kwarewa a rubutu da karatun turanci zai kara wa mutum tagomashi.

Muna so a rubuta takardar nema shiga wannan internship din, dauke da shaidar kammala makarantar sakandare zuwa ga “radiyontalaka@outlook.com”.

Allah Ya baiwa mai rabo sa’a.

Dr. Bello Galadanchi, Managing editor (news & current affairs)                                    

Usman Kabara, Managing editor (programs)

             

Ra’ayoyi 5

Your email address will not be published. Required fields are marked *