Lahadin nan ne shugaban rundunar sojojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun kashe mayakan sa kai na Boko Haram su dubu daya da goma sha biyar a cigaba da aikin dakile al-amuran su a arewa maso gabashin Najeriya da aka fara ranar 12 ga watan Afrilu, wato makonni shida da suka gabata.

Buratai ya bayyana hakan ne a zaman cin abinci da aka shirya tare da sojojin “Ofurashon Lafiya Dole” a birnin Maiduguri Lahadinnan.

Ya kuma kara da cewa an kama manyan shugabanni da ‘yan liken asiri da masu safarar kaya na ‘yan ta’addar su tamanin da hudu duk a cikin wannan lokaci.

Yace “mun mayar da hankali sosai akan mayanan Boko Haram, mun ci galabar su sosai”.

“Mun yi nasarar matsa musu lamba har sai da suka sauya sansani”.

Daya daga cikin manufofin Gwamnatin Buhari shine murkushe ‘yan ta’adda, amma ya zuwa yanzu, wato shekaru biyar kennan da hawan shugaban, ana cigaba da fuskantar kalubale daga mayakan sa kai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *