Ofishin Kiwon Lafiyar Jiha na Bauchi (PHCDA) ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kashewa kowani majinyacin Korona na kwanon abinci daya.

Dr Rilwani Mohammed, wanda shine shugaban Ofishin, shine ya bayyana hakan a tattaunawa da yayi manema labarai a garin Bauchi Lahadinnan, inda yace Gwamna Bala Mohammad ya bada umarnin a tabbatar majinyatar COVID-19 na samun abinci sosai.

Mohammad wanda shine shugaban kwamitin bin diddigin wadanda suka gana da masu COVID-19 ya bayyana cewa ana aiwatar da hakan ne saboda marasa lafiya su saki jikinsu, kuma su nutsu domin gujewa zanga-zanga irin wanda ake gani a wasu jihohin.

A cewar shi “muna kashewa kowani mutum daya nera dubu hudu da dari biyar a kowace rana”.

Irin wannan yanayi ya saka jama’a da yawa suna kiran hukumomi a jihar, domin a kaisu asibitocin da ake tsare wadanda ake zato suna dauke da cutar saboda suma su ci kaza, da kwai da soyayyen dankali.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *