An kori manajan TCN wato (Transmission Company of Nigeria) a turance, ko kuma kamfanin samar da wutar lantarki Usman Gur Mohammed, saboda wata harkar dala biliyan biyu ko nera biliyan dari bakwai da tamanin da daya da shugaban kasa ke jagoranta a karkashin kamfanin Siemens.

Takardar da ta amince da korar, wadda ‘yan jarida suka dora hannun su akai, shugaba Buhari ya saka mata hannu tare da shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.

An kori Mohammed ne a makon da ya wuce sannan aka sauya shi da Injiniya Sule Ahmed a matsayin shugaba mai rikon kwarya. Ministan harkokin makamashi, Injiniya Sule Mamman wanda ya amince da sauyin shugaban cin ya samu iko daga wajen shugaban kasa domin zaben mambobin kwamitin zartaswa na kamfanin samar da wutar lantarkin.

Dama wannan kamfani ya kwan biyu ba tare da kwamitin zartaswa ba tun shekasra ta 2014, tun bayan da tsohon shugaban ta, Marigayi Haman Tukur yayi murabus saboda rashin amincewar shi da yadda abubuwa ke tafiya a bangaren wutar lantarki na Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *