Asusun Lamuni na Duniya (IMF) yayi kiyasin cewa Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirka zasu yi asarar sama da dala biliyan dari biyu na kudaden shiga a karshen shekata ta 2020 saboda annobar Korona.

Shugaban masu bincike akan cigaban nahiyar Afirka, Mr. Papa N’Diaye, wanda ya wallafa rahoton bincike akan yanayin tattalin arzikin yammacin Afirka shine ya sanar da hakan a sautin yanar gizo da ya fitar Lahadinnan.

Ya kara da cewa a shekata ta 2019, wannan yanki yayi asarar misalin dala biliyan 100, inda ya jaddada cewa rashin cimma nasara wajen dakile yaduar kwayar cutar Korona zai kawo babban kalubale ga bangarorin kiwon lafiya da ma tattalin arzikin wannan yanki.

Bisa yadda mawallafin yayi biyani, yankin yammacin Afirka na fuskantar babban kalubale dake kokarin dawo da hannun agogo baya akan cigaban da aka samu a shekarun da suka gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *