Dakarun Sama dake gudanar da aiki mai taken “Operation Hadarin Daji” sun bayyana cewa sun jibgi ‘yan bindiga a jihohin Katsina fa Zamfara tsakanin Mayun 20 zuwa 22 inda suka kashe dari da talatin da biyar har lahira. 

Wanda ke da alhakin wannan aiki ta bangaren yada labarai Manjo Janar John Enenche ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanonin maharan. 

Ya kuma kara da cewa an kai hare haren ne biyo bayan bayanan sirri da suka samu dangane da inda maharan suke. 

Daga cikin sansanonin yace akwai Abu Radde, da Dunya dake Jibiya da karamar hukumar Dan Musa, da sansanin Hassan Tagwaye da na Alhaji Auta dake kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a Jihar Zamfara. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *