A ‘yan kwanakin baya ne cikin azumin bana, wani bidiyo da kuma murya suka dinga yawo a shafukan sada zumunta da a ka yi imanin Malam Bello Yabo ne ke ragargazar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i kan hana sallar jam’i a yaki da cutar Korona.

Shaikh Bello Yabo, Malamin Islama a Sakkwato

Shedun da suka bukaci mu sakaya sunansu sun bayyana mana cewa an kama Malamin ne a ranar Juma’a da ta gabata bayan sallar la’asar a garin nasu tare da zarcewa da shi zuwa jihar Kaduna da a ke sa ran a nan zai fuskanci Kuliya manta sabo. Shedun suka ce jami’an tsaro ne cikin kayan gida suka sami Malamin tare da nuna masa shedar kamu daga wata Kotu a Kaduna, inda shi kuma Malam ya bi jami’an ba tare da cewa kanzil ba.

Ga wadanda suka ji murya ko suka kalli bidiyon wa’azin Malamin da a ke zaton a watan azumin shekarar nan ta 2020 yayi ya kuma dinga yawo a shafukan sada zumuntar zamani. An ji Malamin yana bayyana cewa Malaman Kaduna sun ji kunya tunda suka gaza sabawa dokar Gwamna El’rufa’i da ya kakaba na hana al’umma zuwa wuraren ibadu da sunan ana yaki da cutar Korona. 

Daga karshe cikin fushi Malamin ya kira Gwamnan da sunan ‘Dan Tsuntsu’ wanda bai wuce wani ya kwashe shi da mari ba. Ya kuma kara da cewa da a Kaduna yake da Malam Nasir ya ga yadda a ke saba doka, ko kuma a kai wa jihar Sakkwato aron gwamnan a matsayin mai mulki ya sha mamakin yadda za su yi rugu-rugu da dokar da yasa.

Malam Bello Yabo dai ya sha kamu a baya, don hatta tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya taba damke Malamin bisa kausasan kalamai makamantan wadannan. Duk wadanda muka so jin ta bakinsu a bangaren Gwamnati da na mukarraban Malamin game da halin da a ke ciki ya ci tura.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *