Shugaban darikar Shi’a ta jihar Zamfara Sidi Manniru ya bayyana cewa sun ga watann Shawwal kafin yanke shawarar gudanar da Sallar Idi yau dinnan.

A tattaunawa da yayi da ‘yan Jarida, Sidi Manniru ya bayyana cewa an bi dokokin da ake bukata domin tabbatar da ganin wata da shirya Sallar Idi, musamman daga ‘yan darikar a garuruwan Yabo da Illela, da garin Dukkuma dake karamar hukumar Isa.

Da aka tambaya ko kungiyar ta bayyana wa Sarkin Musulmi bayanin ganin watan, cewa tayi a shekaru ashirin da suka gabata, ‘yan Shi’a suna amfani da nasu dokokin ne wajen ganin wata, ba na watan azumi ba kawai kamar yadda suka koya daga shugaban su Shiekh Ibrahim Zakzaky domin gujewa rikicewa a lokutan karshen azumi.

An ga hotunan Sallolin Idin da kungiyar da gudanar a shafukan yanar gizo, batun da ya jawo ce-ce ku-ce.

Manniru ya kara da cewa “mun sanar da wannan lamari ga duka ‘ya’yan kungiyar mu”.

Ya kara da cewa Sallar Idin bai saba sharrudan da gwamnati ta gindaya ba, saboda sun bi shawarwarin da aka bayar domin rufe wuraren ibada saboda rage yaduwar COVID-19.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *