Gwamnatin kasar Kanada ta hana jirgin Najeriya mai suna Air Peace sauka domin kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar.

Wannan ya zo ne bayan share makonni inda aka hana jirgin damar sauka a kasar Kanada.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Air Peace a matsayin jirgin da zai mayar da ‘yan Najeriya gida daga Kanada, da shirin kwasar jama’a daga biranen Toronto da Calgary.

Amma masu bayani sun bayyana cewa ofishin gwamnatin Kanada na kokarin sasantawa da wasu kamfanonin jiragen saman, a kokarin su na hana Air Peace damar gudanar da wannan aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *