Gwamnatin Jihar Kaduna tayi barazanar duk wani ma’aikacin kiwon lafiy da ya gagara zuwa wajen aiki, tana mai cewa tana kallon hakan a matsayin watsi da aiki.

Gwamantin Jihar, a martani da ta baiwa sanarwar yajin aiki da ma’aikatan kiwon lafiyan suka bayar dangane da zabtare albashin su da kaso ashirin da biyar cikin dari, tace babu wanda ya isa yayi mata zagon kasa, kuma ta umarci duka ma’aikatan kiwon lafiya akan su shigar da bayan su ga ma’aikatar kiwon lafiyar da suke wa aiki.

Kungiyar ma’akatan kiwon lafiyan sun baiwa gwamnatin jihar lokaci na dawo musu da kaso 25 cikin dari na albashin su da aka zabtare a watan Afrilu da Mayu, sannan ta nemi da a samar wa ma’akata kayan kare kai daga cututtuka masu yaduwa.

Kungiyar tayi barazanar tafiya yajin aiki a cikin mako daya idan gwamnatin Jihar bata biya mata bukata ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *