Wata kotu a Burtaniya Juma’ar nan tayi watsi da karar cin hancin dala biliyan daya da gwamnatin Najeriya ta shigar akan manyan kamfanonin hakar mai na Shell da Eni.

Rahotanni sun nuna cewa alkali Christopher Butcher ya bayyana cewa kotun bata da hurum sauraron wannan kara.

Wannan kara yana daya daga cikin kararraki da yawa da aka shigar dangane da Ciniki mai na Malabu wanda ya tayar da cece-ku-ce, wanda aka fi sani da OPC245.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya dake taka rawa a cikin batun sun hada da tsohon babban Alkalin Kasa kuma ministan Shari’a na kasa Mohammed Adoke SAN, kuma yana fuskantar wasu kararrakin a wasu kotunan Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *