Haka zalika ya hana mukarabban gwamnati gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhar zai gudanar da Sallar Idi a gida tare da iyalansa.

Mai magana da yawun sa, Garba Shehu, a sanarwa da ya fitar Juma’ar nan, ya bayyana cewa an dauki wannan maki ne domin cigaba da bin dokar zama-a-gida a Abuja domin kare rayukan jama’a daga dukkan kalubale.

Ya kara da cewa an yanke wannan shawara ne domin bin umarnin Sarkin Musulmi kuma shugaban Jama’atu Nasril Islam Alhaji Sa’ad Abubakar, inda aka dakatar da gudanar da Sallolin Idi a kasa baki daya domin bin ka’idojin da Kwamitin Shugaban kasa akan kalubalantar Korona ya saka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *