Dan majalisa dake wakiltar Ajaokuta, Idirissu Lawal yayi kira ga gwamnatin Tarayya akan ta dauki matakan gaggawa domin tabbatar da adadin jama’ar kasa domin gudanar da shirye shirye masu aiki.

Lawan wanda daya daga cikin mambobi ne a Kwamitin lura da adadin jama’a ya bayyana cewa bai kamata kasa ta ciga da canki-cankar adadin mutane ba, kuma ana bukatar kirga mutanen kasa a halin yanzu.

Dan majalisar wanda yayi magana bayan gabatar da takardar yin garambawul ga dokokin kirga mutanen Najeriya wanda a baya ya samu wucewar karatu na biyu, ya bayyana cewa hanya mafi inganci na kawo cigaba a Najeriya shine tabbatar da bayanai na hakika akan jama’ar kasa bayan yin sahihin kirge.

Idirissu yace “akwai matukar muhimmanci mu gudanar da sabon kirge, saboda wanda aka yi a baya shekara ta 2006 ne. Shekaru goma sha hudu, ai da jimawa. Hakan bai kamata ba da har ta kai bamu san yawan mutanen dake kasar nan ba, sai ta kiyasin kasashen waje.”

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *