Sheikh Tukur Adam Al-Manar, Kaduna Najeriya

Shahararren Malamin addinin Musulunci da ke jihar Kaduna Sheikh Tukur Adam Al-Manar ya bayyana mana muhimmancin bada zakkar fidda kai bayan an dire watan Ramadan. Inda Malamin ya fayyace manufar fidda kai bisa manufofi uku zuwa hudu.

Na daya, cike gibin da mai azumi ya rasa a lokacin da ya ke azumi, tare da tsarkake shi daga yin wata yasashshiyar magana. Ko kallon da bai dace da idonsa ba ko kuma jin wasu kade-kaden da ba kamata ya ji ba.

Na biyu kuma shine, ana cire zakkar fidda kai a matsayin cimaka ga mabukata, talakawa da fakirai a ranar Idi domin rana ce da kowa ke farin ciki tare da ci da sha musamman masu hali, bai kamata a ce wani matalauci yana bakin cikin ba shi da abin da shi da iyalansa za su ci ba. 

Na uku, zakkar fidda kai tana koya wa Musulmi bada kyauta da kore masa mako, rowa da kankamon damke abinsa. Wadannan guda ukun sune ta bangaren mai bayarwa da wanda a ke ba wa. Sai kuma abu na karshe wato rukuni na hudu.

Ana bayar da wannan zakkar ne don kasancewa wani alama da wani ginshiki na addinin Musulunci ta yadda za a ga ko ina a na ta fitar wa ta hanyar auna wa da ma’aunin mudannabi tare da kidaya wa a gaban yara da manya.

Don sauraron cikakkiyar nasihar Malamin, sai a ziyarci shafukanmu na sada zumunci a Facebook da Instagram.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *