Dangane da dokar zauna-a-gida dake kalubalantar Musulmai da yawa ta fannin gudanar da Sallar Idi, kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta fitar da sharadin yadda za’a gudanar da Sallar a gida.
Filin Idi dake Sharada a Kano, Najeriya. Hoto: Bello Galadanchi

Dangane da dokar zauna-a-gida dake kalubalantar Musulmai da yawa ta fannin gudanar da Sallar Idi, kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta fitar da sharadin yadda za’a gudanar da Sallar a gida.

Sakatare Janar na kungiyar ne Dr. Khalid Aliyu ya bayyana wannan sharadi da Kwamitin Fatwa ya fitar a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, inda ake yi kira ga Musulmai da su gudanar da Sallar Idi a gida tare da iyali, ko kuma mutum shi kadai.

Kwamitin yayi kira da a dakatar da Sallar jam’i a birane da ma wajen gari. Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Sallar Idi na da raka’o’i biyu ne, da takbir guda bakwai a ra’akar farko, a ciki harda takbir din farko.

Sannan za’a karanta Suratul Fatiha, da kuwa kowace Surah, amma an fi so a karanta Suratul A’ala. A raka’a ta biyu kuma, za’a yi Takbir sau biyar.

Daga nan ne za’a karanta Suratul Fatiha da kuma kowace Surah amma an fi so a karanta Suratul Ghashiyah.

Idan a gida za’a yi Sallar Idi, to ba sai an yi Huduba ba.

Duka wadannan sharuddan sun zo ne daga Hadisan Anas Bn Malik a Sahih Bukhari kamar yadda Al-Kharshi da Al-Munah al-Jalil suka bayyana.

Kwamitin JNI ya kuma yi kira da Musulmi da yi taka-tsan-tsan a jihohin da aka yarda suyi Sallar Idi, su kuma saka takunkumi da bin shawarwarin da Malaman lafiya suka bayar.

Ga mutane da yawa a Najeriya, wannan shine lokaci na farko da basu samu damar yin Sallar Idi a jam’i ba kamar yadda suka saba yi a baya, biyo bayan annobar Korona da ta kashe daruruwan dubban mutane a duniya kuma ta kassara tattalin arzikin duniya da zaunar da mutane a gida ba shiri.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *