Kwalejin Sojojin Najeriya a Jaji dake Kaduna ya gayawa mazauna garin akan kar su firgita a lokacin da suke ganin ana safarar sojoji da kayan yaki akan titin Jaji-Labar-Dunki-Wazata dake Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Major Ajemasu Yake Jingina ya fitarwa manema labarai Alhamis dinnan, ya bayyana cewa Kwalejin zai yi atisayen sa na farko a shekara, wanda dama sau biyu kawai ake yi daga ranar 22 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yuni a yankin Jaji-Labar-Dunki-Wazata.

Sanarwar ta kara da cewa wannan atisaye an tsara ta ne domin gwada dalibai dake daukar darasi na 89 akan shugabanci, dabarun yaki da tabbatar da ikon akan yanayin arangama a fannonin yakin gaba da gaba, da ma yakin sunkuru.

“Atisayen zai gwada fahimtar dalibai a yaki da ta’addanci, da dakusar da tarzomar sojojin sa kai. Bugu da kari, daliban zasu yi shela domin ilimantar da mutanen kauyen Bina akan cutar COVID-19 domin bada nawa gudunmuwar ga al-ummar dake saukarsu a wannan atisaye.”

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *